Tuesday, 27 February 2018
Labari Mai Dadi : Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da zata fara biyan sabon tsarin albashi

Home Labari Mai Dadi : Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da zata fara biyan sabon tsarin albashi
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma'aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin bayanin maraba da babban ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Sanata Chris Ngige ya yi jiya Litinin lokacin da yake jawabi a lokacin bikin cikar kungiyar kwadago ta kasa shekara arba'in da kafuwa.

Ministan ya bayyana cewa tuni har shire-shiren tabbatar da sabon tsarin albashin yayi nisa saboda a cewar sa, wannan gwamnatin da kuma shugaba Buhari suna da matukar tausayin ma'aikatan kasar.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya dake a unguwar Villa, babban birnin tarayya Abuja ta bayyana a jiya cewa su fa su shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo batun zarcewa bisa mulki a zaben 2019 ma bai dame su ba.

A maimakon hakan, kamar yadda muka samu daga fadar, an bayyana cewa su shugabannin kawo yanzu ba abun da ke a ran su irin tabbatar da samun cigaba mai dorewa a kasar tare kuma da jin dadin 'yan Najeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: