Monday, 26 February 2018
Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Inji Halima Ibrahim

Home Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Inji Halima Ibrahim

Harkar fim ta fi rayuwar jami'a wahala - Halima Ibrahim

- Ta kuma siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa

- Ta ce ta koyi hakuri tare da zama da mutane Daya daga cikin sabbin fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood da ke da hedikwatar ta a garin Kano mai suna

Halima Ibrahim ta siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa da dama.

Haka zalika jarumar ta kara da siffanta harkar fina-finan da cewa ta fi ta rayuwar jami'a wahala ta ko wane bangare musamman ma dai yadda mutum zai yi gogayya da jaruman da suka kware kuma duniya ta san su.

Jarumar dai ta yi wannin kalamin ne yayin da take zantawa da majiyar mu ta mujallar Fim inda ta bayyana cewa ita ma tabbas ta koyi darussa da dama tun daga shigar ta masana'antar tare kuma da sauran ilimin zaman rayuwa.

Majiyarmu ta samu cewa jarumar ta kara da cewa shigowar ta masana'antar ta sa yanzu ta koyi hakuri tare da zama da mutane kasantuwar yanzu ta kan yi mu'amala da jama'a da dama kuma daga fannonin rayuwa iri daban-daban.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: