Monday, 5 February 2018
Gida Biyu Maganin Gobara Irin Wasu Shahararun Jaruman Kannywood ke Yi Bayan Sana'ar Fim

Home Gida Biyu Maganin Gobara Irin Wasu Shahararun Jaruman Kannywood ke Yi Bayan Sana'ar Fim
Ga wasu daga cikin manyan jarumai na masana'antar da kuma irin kasuwancin da suke yi bayan fitowar su a fina-finai;

Wasu daga cikin jarumai na masana'antar Kannywood basu dogara da harkar fim kadai wajen neman arziki. Da yawa suna gudanar da wasu harkar kasuwanci domin biyan bukatun su na yau da kullum.

Wannan ya nuna cewa suma dai yan kasuwa ne kuma idan da hali kuna iya ziyartar shagon su ko farfajiyar inda suke gudanar da kasuwancin tasu.
Ga wasu daga cikin manyan jarumai na masana'antar da kuma irin kasuwancin da suke yi bayan fitowar su a fina-finai;

Rahama Sadau

Ita ma Jaruma Rahama Sadau  ba'a baro ta baya wajen nema. Kamar sauran abokan aikin ta ita ma tana da gidan kwalliya na mata irin ta zamani wanda ke garin Kaduna mai suna Sadau Beauty Lounge . Bayan haka akwai kamfanin Sadau pictures wanda ke daukar nauyin shirye-shiryen nishadantarwa duk cikin abubuwan kasuwanci da take yi. Wannan kasuwancin nata ana iya cewa ya zamanto na iyali domin yan uwanta ke tafiyar da kasuwancin.Hassan Giggs

Kuna iya kiran wannan fittaccen mai bada umarni mai ruwa ko kuma dan garuwa amma irin ta gorar roba. G Nature , ruwan sha ne wanda ake durawa a cikin goran ruwa kuma babban direkta
Hassan Gigggs ke da kamfanin. Banda ruwa, kamfanin tana sarrafa lemun sha kala-kala. Ga masu bibiyan shafukan shi zaku shaida cewa Hassan Giggs baya rowan bada ruwan kamfanin shi ga abokan huldar shi har ma da masoyan shi.Maryam Booth

Masoyan Maryam da ma masu bibiyan shafin ta na kafafen sada zumunta sun san cewa wannan jarumar bata wasa da sana'ar da take. Ita kanta bata boye aikin da take yi bayan fim. Tana da shago inda akemwa mata kwalliya irin ta zamani wato Makeup kuma tana sayar kayan kwalliyan mata da kayan sawa. Maryam Booth  kwararriyar mai kwalliya ce kuma bata boye basirar yi ma mata kwalliya indai har an tuntube ta.
Shagon ta Maryam Booth beauty parlour and Collection yana nan garin Kano.Isa A Isa

Wannan babban mai shirya fim kuma jarumi ya dade yana gudanar da kasuwanci shi. Wanda ya shirya fim din Safara kuma ma'ajin kungiyar yan wasan kwaikwayo na hausa, shine shugaban kamfanin I A I travel agency kamfani dake daukar dawainiyar masu neman tafiya kasashen waje. Bayan haka yana da shagon sayar da kayan sawa irin ta zamani mai suna Queen Nabila Boutique kana shine shugaban kamfanin I A I entertainment and film production wanda ke daukar nauyin shirin fim.
Hadiza Aliyu Gabon

Jaruma tana daya daga cikin jarumai mata dake kokarin wajen nuna kasuwancin ta. Jarumar tana da gidan kwalliya mai suna Hadiza Gabon Beauty salon wanda yake titin wharf road dake garin kaduna.

Halima Yusuf Ateete

Jaruma halima ateete itama na daya daga cikin jarumai da na kama sana'a wanda tana da kamfanin popcorn (Gurguru) sunan kamfanita shine A One milk popcorn wanda shagonta na No. 34 opp. Adobayero mall (shoprite) kano state nigeria.


  • Hausaloaded.com na taya su murna da kuma fatan alkhairi 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: