Monday, 12 February 2018
Gane Mini Hanya Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

Home Gane Mini Hanya Jarumi Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe

- Laifin jarumin shi ne ya alkawarta masu zai zo ne da karfe 2:00 na rana amma bai zo ba sai wajen karfe 5:30 na yamma

Labarin da mu ke samu daga majiyar mu ta tabbatar mana da cewa shahararren dan fim din Hausa din nan na masana'antar Kannywood, fitaccen mawaki kuma, mai bayar da umurni a masana'antar watau Adam A. Zango ya sha ruwan duwatsu a garin Gombe dake a Arewa maso gabashin kasar nan.

Mun samu dai cewa Adam A. Zangon dai ya sha ruwan duwatsu ne daga masoyan sa da suka yi cincirindo suna jiran isowar sa a wani dan bikin gala da ya shirya masu a jihar amma sai bai zo ba a cikin lokaci.

 Jarumin ya alkawarta masu zai zo ne da karfe 2:00 na rana amma bai zo ba sai wajen karfe 5:30 na yamma lamarin dai ko kusa bai yi wa masoyan na sa da suka dade suna jiran sa dadi ba.

Mun samu cewa hakan ne ma ya sa sukayi ta yin jifa tare da ayyana kalaman 'ba ma so' wanda hakan ne ma ya sa ba'ayi taron ba har sai idan kura ta lafa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: