Saturday, 17 February 2018
Duniya Makaranta: Hotunan Wata kyakkyawar Macen Soja Ta Shirya Auren kanta Da kanta A Kasar America

Home Duniya Makaranta: Hotunan Wata kyakkyawar Macen Soja Ta Shirya Auren kanta Da kanta A Kasar America

Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama

 Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika

Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama da ba mahalukin da ya taba kai karshen su har ya koma ga mahaliccin sa. Haka nan kuma abubuwan mamaki a kullum faruwa suke ta yi.
Yau ma kuma gamu dauke da wani labarin ban al'ajabi, mamaki da kuma takaici ma a wajen wasu inda muka samu cewa wata kyakkyawar macen soja ta sha alwashin auren kan ta da kan ta.

Ita dai wannan macen mai suna Shaunice Safford tana kuma da adreshin dandalin sada zumunta na Instagram ne (@drsafford) inda ta kudruri aniyar cigaba da wanzar da rayuwar ta tare da ita kanta din bayan auren da ta yi.A cewar ta, Macen sojan Shaunice Safford ta bayyana cewa ba tun yanzu ba ta dade tana muradin ranar da zata yi aure ta zauna cikin kwanciyar hankali da lumana amma hakan bai samu ba sai a ranar 14 ga wannan watan da muke ciki.

Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika kuma rayuwar ta ta kammala cika da farin ciki da jin dadi, hade da walwala.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: