Wednesday, 28 February 2018
Duk Dan fim din kannywood da yake Zagin Buhari dan Maula ne inji Mawaki Saeed Nagudu

Home Duk Dan fim din kannywood da yake Zagin Buhari dan Maula ne inji Mawaki Saeed Nagudu

Mawaki a masana'antar film din hausa na kannywood Saeed Nagudu ya kwancewa yan'uwansa Zani a Kasuwa, Inda yayi kakkausar Suka ga yan film akan zagi ko aibata Shugaban kasa da wasu yan fim suke yi. Ga abinda mawakin yake fadi:

" Da yawa daga cikin irin su suna zuwa Abuja wajen barayin Gwamnanti musamman Gwamnatin PDP da Allah ya kawar da zalincin ta a kasar nan.

Ba za mu hana ku sukar Baba Buhari ba domin kuna da ra'ayi. Amma fa ku sani shi ra'ayi ba hauka bane.

Mene ne laifin Baba Buhari dan ya hana satar kudin talakawan da ake diba a baku a banza?

Shi ne za ku dinga sukar Gwamnanti.

Duk da cewa ra'ayi kowa da irin na shi, amma ni na san da yawan mawaka da yan fim dake sukar Baba Buhari ba mutanen kirki bane wallahi.

Buhari shugaban kasa ne ba wai dan wasan fim ko mawaki ba, kamata ya yi mu wayar da mutane abin kirki ba wai sukar Buhari ba.

A Karshe idan kuna taya iyayen gidanku barayin Gwamnanti sukar Buhari ne, mu ma masoyan shugaban kasa Muhammadu Buhari da muke kannywood ba za mu yi shiru ba shiru mu zuba muku ido ba.

Yadda kuke tutiya 'yan Nijeriya ne ku, mu ma 'yan Nijeriya ne, muna da 'yancin kare Gwamnantin Buhari.

Allah ya karawa shugaban kasa lafiya da daraja. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a Nijeriya baki daya. "

Share this


Author: verified_user

0 Comments: