Thursday, 8 February 2018
Da dumi-dumi: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa

Home Da dumi-dumi: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa
Allah ya yiwa wata surukar shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Mamman, rasuwa.

Maragayiya Hajiya Aisha Mamman ta rasu ne safiyar yau Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2018.
Shugaban labarai na karamar hukumar Daura, Alhaji Salisu Haro, ya bayyana wannan rashi a garin Daura.

Ya ce maragayiyar ta cika ne misalin karfe 11:30 na safe a babban asibitin jihar Katsina bayan gajeren rashin lafiya.

Alhaji Haro ya kara da cewa Hajiya Aisha ta kasance uwargidan marigayi Alhaji Mamman Danbaffale, yaya ga shugaba Buhari.

Hajiya Aisha ta rasu ta bar ‘yaya takwas da jikoki. An birne bisa ga koyarwan addinin Musulunci.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: