Saturday, 10 February 2018
Bazan lamunci maganar raini irin wadda Ali Artwork yawa Ali Nuhu da Adam A. Zangoba - Inji Tijjani Asase

Home Bazan lamunci maganar raini irin wadda Ali Artwork yawa Ali Nuhu da Adam A. Zangoba - Inji Tijjani Asase

Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase yayi kira da cewa irin yanayin abubuwan dake faruwa a masana'antarsu ta fim din Hausa ya kamata a manya a cikin masana'antar su duba domin yara basa ganin girman na gaba dasu suna fadin irin magan-ganun raini da basu dace ba.

Tijjani yayi maganane akan abinda Ali Artwork ya rubuta akan Ali Nuhu da Adam A. Zango inda Ali Artwork yace, jaruman suna son mutum yayita musu bauta da basu girma amma basu baiwa mutum hakkin aikin da ya musu yanda ya kama, haka kuma ya zargi cewa fadan cacar bakin da akayi na kwanannan tsakanin masoyan Alin dana Adamu, su biyun sune suka hadashi da gangan dan kawai su gwara kawunan masoyansu.

Tijjani yace maganar bata kamata kuma ya kamata manya su kula domin shi idan aka mishi bazai lamunta ba.

Ga abinda yace kamar haka:


Share this


Author: verified_user

0 Comments: