Thursday, 8 February 2018
An Saanta Rikicin Ali Nuhu Da Adam A Zango

Home An Saanta Rikicin Ali Nuhu Da Adam A Zango

Masu iya magana su kan ce "Komai ya yi farko zai yi karshe" kuma duk abin da ya yi tsanani to zai yi sauki.

A yau ne aka kawo karshen takaddamar da ta barke tsakanin fitattun jarumai biyu Ali Nuhu da Adam A. Zango, wanda wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar fim suka shiga tsakanin su don ganin a sasanta su. An yi sasancin ne a ofishin Shugaban Hukumar Tace finafinai Isma'il Na'Abba Afakallahu. Sauran wadanda suka shiga aka yi sasanci da su sun hada da Sani Sule Katsina, Falalu A. Dorayi, Nura Hussaini

Hakan ya kawo karshen takaddamar da ta barke tsakanin mabiyan su wadanda suka rika duddurwa juna ashariya a shafukan instagram tsakanin magoya bayan Ali Nuhu da na Adam A. Zango.

Muna fatan Allah ya kiyaye gaba.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: