Thursday, 1 February 2018
Adam A. Zango ya fadi yawan kudin daya samu daga nuna fim din Gwaska ya Dawo

Home Adam A. Zango ya fadi yawan kudin daya samu daga nuna fim din Gwaska ya Dawo

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya bayyana yawan kudin daya samu a ranar farko da aka nuna sabon fim dinshi me suna Gwaska ya Dawo. Adamun yace ya samu naira dubu dari hudu da arba'in da biyu ne.

Ranar farko da aka fara nuna fim din a gidan sinima dake Ado Bayero Mall, Kano, mutane sunyi turuwa don gego kwarkwatar idanunsu, rahotanni sun nuna cewa har daga kasar Ghana mutane sunzo kallon fim din na Gwaska ya Dawo

Share this


Author: verified_user

0 Comments: