Tuesday, 6 February 2018
Adam A. Zango ne ya fara sakani a fim Duniya ta sanni:Yamin abinda bazan taba mantawa dashiba - Fati Shu'uma

Home Adam A. Zango ne ya fara sakani a fim Duniya ta sanni:Yamin abinda bazan taba mantawa dashiba - Fati Shu'uma

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Shu'uma ta fito ta bayyana iri halaccin da Adam A. Zango ya mata kamar yanda ya bukata, Fati tace ta sanadiyyar Adamun ne aka santa domin shine ya fara sakata a fim har tayi suna.

Fati ta kara da cewa abinda kuma Adamun ya mata wanda ba zata taba mantawa dashi ba shine, lokacin da mahaifiyarta ta rasu, Adamun yazo ya zauna aka rika karbar gaisuwa dashi, tace wannan abu ba karamin dadi ya mata ba, hatta 'yan gidansu sunji dadin hakan kuma ba zata taba mantawa dashiba.

A karshe tace bata ma san da wace irin kalma data godewa Adam A. Zango ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: