Sunday, 11 February 2018
Abinda Ba'a Sani ba Game da Arzikin da Ummi ZeeZee take dashi

Home Abinda Ba'a Sani ba Game da Arzikin da Ummi ZeeZee take dashi

Ummi Ibrahim, wadda aka fi sani da Zee-Zee, wadda a yanzu idan aka kira ta da biloniya babu wata matsala, idan aka yi la’akari da irin manyan motoci da yanayin yadda take rayuwa mai dan karen tsada a yanzu. Babu shakka za a iya cewa ta kere wa sa’anninta da dama da suka shiga harkar fim tare a ba

Bayan tsohuwar jarumar wadda ‘yar kabilar Shuwa ce daga jihar Borno, ta dan fito a finanan Hausa da kuma matsalar da ta samu da saurayin da ya yi niyyar aurenta, wato Dan Chana, sai ta yi bulaguro zuwa jihar Lagos, inda ta koma can da zama. Bayan ta koma jihar Lagos da zama ne, Ummi Zee-zee ta soma soyayya da fitaccen mawakin Turancin nan, wato Timaya, inda har ta bayyana cewa tana da burin aurensa idan har ya amince zai Musulunta, amma daga baya sun rabu.

Soyayyar Timaya da tsohuwar jarumar finafinan Hausan, ya yi matukar daukar hankalin jama’a musamman na yankin Arewa kasancewar a matsayinta na Musulma tana soyayya da wanda ba addininsu daya ba, amma daga baya sai ta fito ta wanke kanta da zimmar cewa za ta aure shi ne idan har ya amince zai musulunta.


Sai dai daga bisani bayan an rasa ina soyayyar Zee-zee da Timaya ta kwana, kwatsam sai labari ya soma yaduwa na cewa tuni jarumar suka raba gari da mawakin. Wanda kuma bincike ya nuna cewa tun daga wannan lokacin ta yi bulaguro daga jihar Lagos ta dawo yankin Arewa, inda ta koma jihar Kaduna, inda take zama a kawataccen gida, sannan duk inda za ta tare da masu tsaron lafiyarta take zuwa.

A yayin da al’umma suka soma mancewa da batun Zee-zee, kwatsam sai fitacciyar Mujallar nan ta Fim da jaridar Turanci ta Blueprint suka yi hira da ita, inda a hirar ta ce akwai soyayya mai karfi tsakaninta da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kuma tana sa ran za su yi aure nan ba da jimawa ba.

Idan ba a manta ba, a farkon shekarar da ta gabata, wani na kusa da jarumar, ya fadawa majiyarmu cewa Ummi Zee-zee ta sha fiya-fiya don ta kashe kanta, sakamakon matsalar da ta samu da janar Babangidan, wanda har ta kai ga janar din ya kashe duk wasu lambobin wayoyinsa da ya sa jarumar za ta same shi, kuma ya hana ta mu’amala da duk wasu kadarorinsa da ke jihohin Kano, Kaduna, Niger har ma da na kasashen waje.

Kasancewar Zee-zee tana bukatar janar Babangidan ya san irin halin da ta shiga sakamakon matsalar da suka samu, sai ta bayyana a jaridar Blueprint kan yadda ta yi kokarin halaka kanta ta hanyar shan fiya-fiya, inda bayan an buga labarin wani na kusa da ita, ya kira majiyarmu yake cewa Janar din ya kira ta, kuma har ya tura tawaga zuwa Kano domin duba lafiyarta, ko da bukatar a haura da ita kasar waje domin duba lafiyarta.

Majiyarmu ta ci gaba da cewa tun daga wannan lokaci, a duk sanda aka nemi Zee-zee aka rasa, idan aka tambayi makusantan jarumar, sukan bayyana cewa walau ta wakilci Janar din a wurin taro a fadin kasar nan, ko kuma ta wakilce shi a harkokin kasuwancin da yake gudanarwa a kasashen waje.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: