Saturday, 10 February 2018
Abin Arziki Rahama Sadau Kannywood ta samu Sabuwar Sarauniya

Home Abin Arziki Rahama Sadau Kannywood ta samu Sabuwar Sarauniya
Shaharren mai hoto George Okoro ya karrama ta bisa kokarin da take harkar nishadantarwa da kuma gudummawar da take bada wa ga sauran matasa


Kada kuyi tunani ko wata balarabiye ce ko sarauniyar Indiya ce, wannan ba kowa bane face  sabuwar sarauniyar Kannywood Rahama Sadau.

Shahararren mai hoto George okoro ya karrama jarumar fim bisa rawar da take takawa a harkar fim tare da irin taimakon da take wajen zuga sauran matasa wajen cinma burin su a rayuwa.

Ya bayyana hakan ne a shafin shi na Instagram jiya juma'a 9 ga wata 2018.


 Rahama Sadau tayi ado irin ta yan  sarauta  (instagram/Georgeokoro)
Mai hoton wanda yake takama da sarautar "Sarkin masu hoton galadiman zazzau" ya shahara ne a fannin daukan hoto kuma yana daya daga cikin manya da ake damawa dasu a harkar.

Idan baku manta ba, duk da kalubalen da ta fuskanta wannan jarumar bata yi jinkiri ba wajen cigaba da nuna basirar ta a harkar nishadantarwa ba kuma bata yi sakaci ba wajen neman hanyar dazata bi wajen cinma burin ta. Jarumar wanda ta shahara a farfajiyar Kannywood Ta samu damar fitowa a fina-finai da dama a masana'antar nollywood dake kudancin kasa wanda yasa a yanzu ana jin duriyarta a ko wani yanki na kasar.

Bugu da kari da Kari shirin fim na farko wanda ta shirya da kanta wato "Rariya"ya samu lambar yabo shirin fim mafi burgewa daga arewacin Nijeriya na kyuatar City people awards a nan jihar Legas  bara.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: