Wednesday, 6 September 2017
‘Yan Boko Haram Sun Kashe Manoma Biyu, Sun Sace Biyu

Home › › ‘Yan Boko Haram Sun Kashe Manoma Biyu, Sun Sace Biyu

WASHINGTON D.C. — Wasu da ake
kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun
shiga wani kauye mai suna Alau mai
tazarar kilomita biyar daga Maiduguri,
babban birnin jahar Borno, su ka yi ma
wasu manoma biyu yankar rago su ka
kuma sace wasu biyu.
Tashin hankalin da ya biyo bayan wannan
al’amari ya sa wasu magabatan wannan
gari, bisa jagorancin wakilin Lawanin
garin, sun ruga birnin Maiduguri inda su
ka tuntubi hukumomi da ‘yan jarida.
Wakilin Lawanin garin mai suna Babakura
Lawan, ya gaya ma manema labarai cewa
ba a san inda aka kai wadanda aka sace
din ba. Ya ce wadanda aka kashe din su ne
Bulama Musa da Madu Abba Musa
Gulumba kuma manoma ne da aka sansu
sosai a garin.
Wakilin Bulaman ya ce tun ba yau ba ake
ta gaya ma hukumomi yanayin tsaro a
yankin ba tare da an dau wani mataki ba.
Ya ce wani sa’in ma har kama mutane ake
yi a je a zuba su cikin kwale-kwale a
watsar da su cikin ruwa. Shi ma Kansilan
wurin, wanda aka sakaya sunansa, ya ce
rabin kayan abinci da ake kaiwa birnin
Maiduguri daga kauyen na Alau su ke
fitowa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: