Sunday, 10 September 2017
Yadda ake musguna wa Musulmin Rohingya

Home › › Yadda ake musguna wa Musulmin Rohingya
Akalla Musulmai 'yan kabilar Rohingya 290,000
daga jihar Rakhine a kasar Myanmar suka
ketara zuwa kasar Bangladesh mai makwabta
cikin makonni biyu da suka wuce.
Musulmin 'yan gudun hirar na cewa sojojin
Myanmar su na kona kauyukansu- zargin da
sojojin ke musantawa.
Tashin hankalin ya fara ne a ranar 25 ga watan
Agustan da ya gabata lokacin da wata
kungiyar gwagwarmayar 'yan Rohingya ta kai
wa wani ofishin 'yan sanda hari a arewacin
jihar Rakhine.
Daga nan ne sai sojojin Myanmar suka fara
murkushe su, kamar yadda 'yan kabilar
Rohingya suka bayyana.
Sai dai gwamnatin kasar ta musanta hakan,
inda ta ce ta na yakar "'yan ta'addan"
Rohingya ne kawai.

'Yan Rohingya wadanda galibinsu Musulmi ne
da ba su da kasa, na rayuwa ne a kasar
Myanmar wacce mabiya addinin Buddha ke da
rinjaye.
Kungiyoyin ba da agaji a Bangladesh sun ce
adadin 'yan gudun hijirar Rohingya da ke shiga
kasar ya wuce wanda za su iya dauka, yayin
da ake cewa akwai dubban 'yan Rohingya da
ke tsaye a gefen hanya, suna rokon abinci.
Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AP
ya ce, ya hangi wani mutum da ya yanke jiki ya
fadi yayin da yake bin layin abinci.
Har ila yau, wani wakilin BBC ya ce a kan
idonsa aka cinnawa wani kauyen Musulmin
Rohingya wuta a jihar Rakhine da ke Myanmar.
Ana ci gaba da yin kalaman Allah-wadai game
da yadda gwamnatin Myanmar ta ke
musgunawa Musulmi tsiraru 'yan kabilar
Rohingya.
Mawuyacin halin da Musulmin ke ciki ya sa
ana sukar Shugabar Kasar Aung San Suu Kyi
kan yadda ta ki ta kare su daga musgunawar
da suke ci gaba da fuskanta.
Shugabannin kasashen duniya sun bukaci
Misis Suu Kyi, wadda ta taba lashe kyautar
Nobel ta Zaman Lafiya da ta fito ta yi magana
a madadin 'yan Rohingyan.
Koda yake ta amsa kiran daga bisani, inda ta
ce "kafofin yada labarai na kara gishiri game
da abin da yake faruwa a jihar Rakhine."
Daga nan ta ce "ana kula da duk wani mutum
da yake zaune a Myanmar dan kasa da kuma
bako, muna iya kokarinmu duk da cewa ba mu
da wadata sosai."
Tarihin kabilar Rohingya
Akwai kimanin 'yan kabilar Rohingya miliyan
daya da dubu dari uku a Myanmar, yayin da
kuma wadansu miliyan daya da rabi suke
rayuwa a wadansu kasashen duniya galibinsu
'yan gudun hijira ne.
Yawancinsu Musulmi ne, kodayake akwai
wadansu tsiraru daga cikinsu da ke bin addinin
Hindu.
Majalisar Dinkin Duniya ta taba bayyana su a
matsayin al'ummar da tafi fuskantar
tsangwama a fadin duniya.
A shekarar 1982 ne gwamnatin kasar Myanmar
ko kuma Burma ta kirkiri wata sabuwar doka
wadda ta hana wa 'yan Rohingya damar su ta
kasancewa 'yan kasa.
Gwamntin Myanmar tana cewa su ba 'yan
kasarta ba ne, 'yan cirani ne daga kasar
Bangladesh.
Duk da cewa kabilar tana cewa ta samu asali
ne tun a karni na takwas, amma gwamnatin
kasar ba ta daukarta a matsayin daya daga
cikin dimbin kabilun kasar.
A Myanmar an takaita wa 'yan Rohingya damar
zirga-zirga da neman ilimi da kuma damar yin
aikin gwamnati, kamar yadda kungiyar kare
hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta
bayyana.
Ba bana ne karon farko da 'yan Rohingya suke
fuskantar wannan musgunawar ba.
Musulmin Rohingya sun fuskanci musgunawa
daga sojojin Myanmar a shekarun 1978 da
1992 da 2012 da 2015 da 2016 da kuma
2017.
Wanne taimako yanzu haka suke samu a wajen
kasashen Musulmi?
A ranar Asabar ne Farai Ministan Malaysia
Najib Razak ya ce 'yan kabilar Rohingya suna
"fuskantar azabtarwa da fyade da kuma kisa."
Ya ce abin kunya yadda gwamnatin Myanmar
ta ki yin komai game da al'amarin.
Hakazalika, gwamnatin Pakistan ta ce ta kira
jakadan Myanmar da ke kasar a wani mataki
na "nuna rashin amincewa da farmakin da ake
kai wa Musulmin Rohingya."
A makon jiya an rika samun jerin zanga-zanga
a kasashen Indonesiya da kuma Indiya, inda
ake Allah-wadai da gwamnatin Myanmar.
Sai dai sauran manyan kasashen Musulmi
kamarsu Saudiyya da Masar da kuma Iran ba
su ce komai ba tukuna.
Hukumomin kasar Bangladesh sun ce suna
zargin dakarun gwamnatin Myanmar da binne
nakiyoyi a kan hanyar da 'yan gudun hijiran
Rohingya ke bi, suna tserewa daga kasar.
Bangladesh ta kira jakadan Myanmar da ke
kasar don nuna rashin jin dadinta. Sai dai
gwamnatin Myanmar ta musanta aika ta
hakan.
Mene ne gaskiyar hotunan da ake yada wa a
kafafen sada zumunta?
Tun bayan fara rikicin ne na kwana-kwana nan
ne ake samun labarai da hotuna da kuma
bidiyo musamman a kafafen sada zumunta
wadanda suke ikirarin nuna musgunawar da
Musulmi 'yan kabilar Rohingya ke fuksanta a
Myanmar.
Sai dai galibin wadannan labaran da hotunan
ba gaskiya ba ne.
Yawancinsu na wadansu rikice-rikice ne ko
tashe-tashen hankula da suka faru a wani wuri
a baya can, amma ba a Myanmar ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: