Friday, 8 September 2017
Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu

Home › › Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu

An tsinci gawar wata matashiya da ta fara
rubewa mako guda bayan da wani mai maganin
gargajiya ya mika kansa ga 'yan sanda ya ce ya
gaji da cin naman dan adam.
Mutanen yankin KwaZulu na cike da fargaba
bayan da aka gano gawar Zanele Hlatshwayo
mai shekara 25, an ciccire wasu sassan jikinta,
a kuayen Shayamoya a Afirka Ta Kudu.
Iyayen yarinyar wacce ta bata tun a watan
Yuli, sun yi amannar cewa tana daga cikin
wadanda masu cin naman mutane ne suka
kashe, inda tuni aka kama biyar daga cikinsu.
Da farko dai 'yan sanda sun ki saurarar batun
mutumin da ya mika musu kan nasa, amma
sai suka yarda da abin da yake fada a lokacin
da suka ga jini dumu-dumu a hannayensa da
kafafuwansa, suka kuma kama shi.
Mutumin ya kai 'yan sandan gidansa, inda aka
samu kunnen mutum har takwas a cikin
tukunya.
An yi amannar cewa ya yi niyyar sayarwa
abokan huldarsa ne, wadanda aka shaida wa
cewar suna da sirri na taimakawa mutum ya yi
kudi ko ya samu mulki.
An kuma samu wasu sassan jikin da dama a
wani akwati.
An samu tufafin Ms Hlatshwayo da jini kaca-
kaca a jiki a dakin mai maganin gargajiyar da
aka samu sassan jikin mutanen.
Iyayenta ne suka gane tufafin nata.
Haka kuma, 'yan sansa na jiran sakamakon
gwaje-gwajen kwayoyin halitta domin a
tabbatar ko daga cikin sassan jikin mutanen
akwai na wata mata mahaifiyar wani yaro dan
shekara biyu.
Har yanzu iyayen Ms Hlatshwayo ba su binne
ta ba. A yayin da na shiga gidansu
Hlatshwayo, ba abin da nake ji sai koke-koken
'yan uwanta.
Babbar yayarta Nozipho Ntelele, ta ce min a
lokacin da take share hawaye, "Muna jin ciwon
salon da aka bi aka kasheta, an mata kisan
wulakanci."
Ta kara da cewa, "Duk tufafinta ya yi duku-
duku da dattin kasa, alamar ta sha artabu
wajen ganin ta ceci ranta," "in ji Ms Ntelele.
Warin rubabben naman mutum
Mai maganin gargajiyar na zaune ne a wata
bukka a Rensburgdrift kusa da Estcourt.
Ana kiransa da "Mkhonyovu" wanda
ma'anarsa ke nufin "mai tafka almundahana" a
yaren Zulu na kasar.
Ya karbi hayar gidan ne daga wajen Philani
Magubane, wanda shi ma ake zargin kaninsa
da irin wancan laifin.
"Na kadu matuka da jin cewa kanina ya yarda
da tatsuniyar mai maganin gargajiyar nan, inda
ya yi musu alkawarin arziki bayan kuwa shi
talaka ne futuk," in ji Mr Magubane.
Ya ce daya daga cikin masu zaman haya a
gidan ya yi ta korafin cewa yana jin warin
rubabben nama na fitowa daga gidan
makwabcinsa.
"Mkhonyovu bai fi wata biyu da tarewa a gidan
ba, ban taba sanin cewa yana ajiye sassan
jikin mutane ba saboda ni ba anan nake zama
ba," in ji Mr Magubane.
Mr Magubane ya ce ya tabbata kaninsa da
sauran mutanen sun rudu ne da karairayin mai
maganin da ya ce zai musu tsafi su yi arziki.
Ana zargin cewa yana aika mutane su tone
kaburburan jama'a ne da tsakar dare don ya
hada wani tsafi da ake kira "muti".
Yadda mutane suka ci naman mutum suna
sane
Mthembeni Majola, wani dan siyasa a garin ya
kira taron al'ummar yankin jim kadan bayan da
daka gabatar da masu cin naman mutanen a
gaban kotu.
"Mazauna garin da dama suna zaune cikin
tsoro tun bayan fallasuwar siriin mutanen,
amma Mr Majola ya ce wasu mutanen ba su yi
mamaki ba.
"Wasu da dama sun tabbatar da cewa sun san
abin da mai maganin ke yi har ma sun ci
naman mutum suna sane," in ji shi.
"Amma abin da ya bata mana rai shi ne yadda
mutanenmu suka zama sakarkaru, yawancin
wadanda suke zuwa wajen mai maganin
barayin shanu ne wadanda yake cewa zai ba
su sa'a su dinga bacewa ko ba su maganin
karfe don ko 'yan sanda sun harbe su bindiga
ba za ta same su ba, in ji Mr Majola.
Phepsile Maseko, wata jagora ce a kungiyar
masu magain gargajiya ta Afirka Ta Kudu, ta
kuma yi Allah-wadai abin da masu cin naman
mutanen ke yi.
Ta ce, "Mkhonyovu mai maganin karya ne
wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya
shigo da mugun abu cikin sana'armu.
"Kashe mutane da yin tsafi da sassan jikinsu
ba ya cikin tsarin maganin gargajiya, abin da
ya yi ya bata mana rai saboda a yanzu dole sai
mun fito mun kare aikinmu da kyau gudun
bacin suna," in ji Ms Maseko.
Mutane biyar din da aka kama wadanda aka
gurfanar da su a kotu ranar Litinin sun yi watsi
da belinsu da aka bayar, za kuma su sake
gurfana a gaban kotun a karshen watan
Satumba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: