Wednesday, 6 September 2017
World Cup: Argentina na ci gaba da fafutika

Home › › World Cup: Argentina na ci gaba da fafutika

Argentina ta ci gaba da fafutikar ganin ta samu
gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018
inda ta sha da kyar a hannun Venezuela, wacce
ke mataki na karshe, da ci 1-1 a wasan da suka
yi a gidan Argentinar.
Dan wasan Venezuela Jhon Murillo ya soma
jefa kwallo a ragar Argentina ko da yake
kwallon da suka ci kansu bayan komawa daga
hutun rabin lokaci ta sa Argentina ta samu
maki daya.
Yanzu dai Argentina na matsayi na biyar a
cikin kasashen da ke Kudancin Amurka kuma
suna da sauran wasa biyu yayin da kasashe
hudu da ke suka fi yawan maki suka cancanci
zuwa gasar cin kofin duniyar - Argentina za ta
fuskanci New Zealand.
Brazil, wacce tuni ta samu gurbin zuwa gasar,
ta yi kunnen-doki 1-1 da Colombia.
Dan wasan gaba na Chelsea Willian ne ya ci
wa Brazil kwallo ko da yake daga bisani dan
wasan Monaco Radamel Falcao ya fanshe.
Dan wasan tsakiya na Liverpool Philippe
Coutinho ya shigarwa Brazil wasa bayan an yi
nisa da wasan.
Uruguay tazakuda zuwa matsayi na biyu bayan
ta doke Paraguay da 2-1 yayin da Peru ta buge
Ecuador inda ta zama ta hudu. Chile, wacce ke
matsayi na shida ta sha kashi a hannun
Bolivia da ci1-0.
Chile, wacce ke bayan Argentina da maki daya,
za ta barje gumi da Ecuador kafin ta kammala
wasanta da wacce ke matsayi na daya Brazil a
watan gobe.
Argentina, wacce sau biyu tana lashe gasar
sannan ita ce ta biyu a shekarar 2014, na da
maki daidai da na Peru, wacce za su fafata
nan gaba, kafin su gwabza da Ecuador.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: