Saturday, 9 September 2017
Talauci Da Kuncin Rayuwa Na Sa Matasa Shiga Boko Haram da 'ISIS.'

Home › › Talauci Da Kuncin Rayuwa Na Sa Matasa Shiga Boko Haram da 'ISIS.'

<font color="red"> Kamar yadda tun da ake kyautata zato,
wani bincike ya gano cewa talauci da
kuncin rayuwa na sa matasa shiga
kungiyoyi masu tsauraran ra'ayoyi</font><br>

Talauci da kuncin rayuwa da kuma
amfani da ikon gwamnati ba bisa ka'ida
ba na ingiza matasa a Afirka zuwa cikin
kungiyoyi masu tsauraran ra'ayoyi irin
su Boko Haram da al-Shabab da kuma
ISIS, bisa ga wani binciken Shirin
Wanzar da cigaba na MDD, wanda shi
ne irinsa na farko.
Binciken mai shafuka 124, wanda aka
gudanar cikin tsawon shekaru biyu, ya
ta'allaka ne kan tambayoyin da aka yi
ma wasu mutane 495 masu samar da
sabbin mambobi ma kungiyoyi masu
tsattsauran ra'ayi.
Binciken ya bi diddigin dalilan da su ka
sa matasa a Afirka ke sha'awar shiga
kungiyoyi masu aikata ta'addanci, ya
kuma bayyana yadda ake samun
sabbin mambobin, da jahilcin da ke ciki,
da kuma hadarin da ke dada karuwa,
sannan rahoton binciken ya bayar da
shawarwari kan yadda za a kawo
karshen al'amarin.
"Rahoton ya gano cewa talauci ne ya yi
shinfida ma hanyar shiga kungiyoyi
masu tsattsauran ra'ayi," a cewar
babban jagoran rubuta wannan rahoton
kuma shugaban Shirin wanzar da
cigaba ma MDD (UNDP) shiyyar Afirka,
Mohammed Yahaya. Ya kara da cewa
"Talauci, da danniya da rashin cigaba
na taka rawa sosai a wannan al'amari a
Afirka kuma saboda haka, ya kamata
ma'abuta cigaba su shigo cikin
fafatukar ta neman mafita."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: