Monday, 11 September 2017
Suna Neman Hanyar Hallaka General T.Y Buratai Ko Ta Wane Hali !!!

Home Suna Neman Hanyar Hallaka General T.Y Buratai Ko Ta Wane Hali !!!

Ku fahimci wani abu, bincikenmu yasa mun gano a duk lokacin da General Tukur Y Buratai zai tafi ran-gadi a kananun hukumomin jihar Borno musamman garuruwan da a baya Boko Haram suka kwace, Gen Buratai yakan sanar da wani mutum guda wanda yake da alhakkin ya sani cikin 'yan siyasa a jihar Borno kamar yadda doka ya tanadar cewa zai ziyarci gari kaza

A tsakaninsu su biyu zasuyi maganar batare da kowa ya sani ba, amma da zaran Buratai ya kama hanya sai Boko Haram suyi masa harin kwanton bauna, wannan abu ya faru lokacin da Buratai zai ziyarci garuruwan Gamboru-Ngala, Bama, Munguno da Damboa, duk anyi mishi hari domin a hallakashi, wannan daliline yasa Buratai ya rage ran-gadin da yake kaiwa dakarunshi a Borno, me yasa suke ta kokarin sai sun hallaka shi?

Kamar yadda muka fada a baya kungiyoyin NGOs a jihar Borno suna kallon Buratai a matsayin babban mai kawo musu cikas da matsaloli akan boyayyen ajandarsu na sharri

NGOs sun sayi wasu mukarrabai musamman 'yan siyasa amma Buratai ya gagaresu a yanda bincikenmu ya nuna mana, daga cikin 'yan siyasar Borno da NGOs suka saya kuma yake musu aiki akwai Kadiri Rahis 'dan majalisar Tarayya dake wakiltar Maiduguri

Kuma jama'a ko zaku iya tunawa lokacin da bomb ya tashi a post office area wajen kasuwar 'yan waya wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan matasa dake harkar waya?

Bayan harin bincike ya tabbatar da cewa motar da aka tafi da ita cike da bamabamai motar tana dauke da rejista a plate number dinta wanda ya nuna cewar motar na Kadiri Rahis ne, to kunga wannan mutumi tun kafin ya zama chairman yayi aiki da kungiyar Ecomog wacce take da alaka da NGOs, a yanzu kuma member ne a house of reps

Kadiri Rahis a irin rawar da yake takawane a cikin sha'anin Boko Haram kwanaki aka kamashi tare da Chairman na karamar hukumar Mafa da wani 'dan Shehun Borno da zargin suna da hannu dumu dumu a cikin ta'addancin Boko Haram, amma sai NGOs da wasu manya sukabi aka kashe maganar aka sakesu, babu damar aci gaba da bincikensu saboda 'yan siyasane kuma  'ya'yan manya sunfi karfin hukuma

Don haka indai Buratai zai cigaba da ziyartar dakarunshi dake fagen yaki a cikin mota to babu shakka zasu iya hallakashi a kowani lokaci, don haka hanya mai sauki shine ya dinga tafiya a jirgi kawai, saboda NGOs basa kaunarshi, musamman da ya fito yace musayar 'yan matan Chibok da akayi ra'ayin 'yan siyasa ne ba soji ba, wannan ya bakanta musu rai, don haka zasu farauci rayuwarshi ta kowani hali

Yaa Allah Ka kare mana Gen. Buratai daga sharrin masharranta


Daga:Datti Assalafiy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: