Monday, 11 September 2017
Sojin Najeriya sun karyata farmaki kan 'yan Biafra

Home › › Sojin Najeriya sun karyata farmaki kan 'yan BiafraRundunar sojin Najeriya ta musanta wasu
rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari
tare da kashe mutane a garin Afaraukwu na
madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra,
IPOB, Nnamdi Kanu.
A sanarwar da rundunar ta fitar ta karyata
labarin da kungiyar ta IPOB take yadawa da
ma wasu hotuna na mutane da ake cewa
sojojin sun harba wadanda ake yadawa a
intanet,a lokacin da sojojin suka yi wa kauyen
Nnamdi Kanun dirar mikiya.
A martanin da sojojin suka yi sun ce babu wani
abu makamancin haka da ya faru, illa dai wasu
tsegarun kungiyar ta fafutukar kafa kasar
Biafran ne suka datse hanya ga kwambar
sojojin da ke kewaya birnin Umuahia na jihar
Abia a jiya Lahadi da yamma, har ta kai da
suna jifan sojojin da duwatsu da fasassun
kwalabe, lamarin da ya yi sanadiyyar raunata
wata mata da ke wucewa da kuma wani kofur
na sojin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: