Monday, 11 September 2017
Shakaru 25 Da Rasuwar Shiekh Abbubakar Mahmud Gummi: Taƙaitaccen Tarihinsa

Home Shakaru 25 Da Rasuwar Shiekh Abbubakar Mahmud Gummi: Taƙaitaccen Tarihinsa


Daga Aliyu Ahmad

An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi ne a cikin garin Gumi dake jihar Sokoto, a shekara ta 1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya 1922.

Malam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya
da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin
kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan
zamanin).

Haka kuma marigayi Sheik Gumi ya yi karance-
karance na zaure a majalisi daban-daban na
Malaman da suka shahara a kasar Hausa a
wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi Arabiya.

Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin
binciken Al-kur'ani da Sunna kan hukunce-
hukuncen Shari’a, tun daga abin da ya shafi
Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci, wanda
karantarwar da ya yi ta tabbatar da haka.

Malam ya yi rubuce-rubuce masu yawa, kadan
daga cikin su akwai:- *Al Akeedatus Saheehah bi Muwaafakatish Shari’ah

*Tarjamar Ma’a’nonin Al-kur’ani Mai Girma.
Tafsirin Al-kur’ani:

*Raddul Azhaan ilaa Ma’aanil Kur’an.

*Tarjamar littafin Hadisin “Arba’uunan
Nawawiy”

Littafi mai suna *Manufata” ko (Where I
Stand).

Wannan littafi ya na da matukar amfani ga sanin tarin siyasar kasar nan da ta shafi Addini da Mulki da sauransu.

Sheik Gumi ya rasu ne a ranar 11 ga watan Satumba, 1992.

Allah ya jikan Malam, ya gafarta masa da sauran Musulmi. Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: