Wednesday, 6 September 2017
Ministar Buhari 'ta soma yi wa Atiku kamfe'

Home › › Ministar Buhari 'ta soma yi wa Atiku kamfe'

Ministar harkokin mata ta Najeriya ta soma yi
wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku
Abubakar yakin neman zabe na shekarar 2019.

Hajiya Aisha Jummai Alhassan, wacce ta
jagoranci shugabannin jam'iyyar APC na jihar
Taraba domin kai gaisuwar Sallah ga Atiku
Abubakar, ta yi addu'ar Allah ya ba shi
shugabancin kasar a 2019.

Wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian wacce ake
wallafawa a shafin intanet ta buga, ya nuna
ministar a gaban tsohon mataimakin shugaban kasar tana cewa, "Your Excellency (mai girma), babanmu, shugaban kasarmu idan Allah ya yarda a shekarar 2019... a gabanka, mutanenka ne, magoya bayanka har abada; mutanen jihar Taraba.


"Sun zo gaisuwar ban-girma, gaisuwar Sallah
da kuma yi maka murna ta wannan daukaka
(Wazirin Adamawa) da Allah ya kara maka".

Minista Alhassan ya gabatarwa tsohon
mataimakin shugaban kasar shugabannin
jam'iyyar, tana mai cewa wasunsu sun matsa
domin su yi jawabi a gabansa amma hakan ba
zai yiwu ba saboda ya gaji.


Tawagar ta rika yin tafi a lokacin da ministar ke
wadannan jawabai.


Ministar ta harkokin mata dai ita ce ta yi
takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin
jam'iyyar APC a shekarar 2015, ko da yake ta
sha kaye a hannun Gwamna mai-ci, Darius
Ishaku na jam'iyyar PDP.


Masana harkokin siyasa dai na ganin tsohon
mataimakin shugaban kasar, wanda ya fafata
da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben fitar
da gwani na APC a shekarar 2014, zai sake
tsayawa takara a zaben 2019.


Suna ganin wannan ce dama ta karshe ga
Atiku Abubakar ta zama shugaban kasar,
ganin cewa har yanzu ana tunanin za a fitar da
shugaban kasar ne daga arewacin kasar,
sannan shekarunsa na ci gaba da ja, inda ya
haura shekara 70.


Sai dai suna ganin zai fuskanci babban
kalubale a wurin mutane irinsu su tsohon
gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso,
wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin
na APC a wancan lokaci kuma ake tunanin zai
sake son tsayawa takara, da gwamnan jihar
Kaduna Nasir El-Rufa'i, da kuma shugaban
majalisar dattawan kasar Bukola Saraki,
wadanda ake ganin za su yi takarar
shugabancin kasar.


Kazalika masana siyasa na ganin Atiku
Abubakar zai fuskanci adawa daga tsohon mai
gidansa Cif Olusegun Obasanjo, wanda ake
ganin ba sa ga-maciji da juna.

.
Sun bayyana cewa rashin lafiyar da Shugaba
Buhari, mai shekara 74, ke fama da ita na cikin
abubuwan da ke kara kaimi ga masu son yin
takara a zaben 2019 su fito su bayyana hakan,
alabishi idan ya ce ba zai sake yin takara ba.
Amma har yanzu shugaban bai bayyana
shaukinsa na sake tsayawa takarar ba ko
akasin hakan.


Amma makusantansa sun nuna yiwuwar
tsayawa takararsa a shekarar 2019.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: