Monday, 11 September 2017
Messi ya ci wa Barca kwallo uku a wasa sau 38

Home › › Messi ya ci wa Barca kwallo uku a wasa sau 38A ranar Asabar Barcelona ta ci Espanyol
5-0 a
gasar La Liga wasan mako na uku da
suka kara
a Camp Nou.
A karawar ce Lionel Messi ya ci kwallo uku
rigis, kuma karo na 38 kenan yana yin
haka
tun komawarsa Barcelona da taka-leda a
matsayin kwararren dan kwallo.
Jumulla ya ci kwallo uku sau 27 a gasar
La
Liga da kuma sau bakwai a gasar cin kofin
zakarun Turai da sau uku a Copa del Rey
da
sau daya a Spanish Super Cup.
Karo na uku kenan Messi dan kasar
Argentina
yana cin Espanyol kwallaye uku a wasa,
amma
Valencia ce kungiyar da ya fi cin kwallo
uku
rigis, wacce ya yi wa hakan sau hudu a
tarihi

Share this


Author: verified_user

0 Comments: