Wednesday, 6 September 2017
Mai tsohon ciki ta kashe kanta da jaririnta

Home › › Mai tsohon ciki ta kashe kanta da jaririnta

Wani asibiti a tsakiyar China yana nazari kan
yadda aka yi har wata mai tsohon ciki da ke
nakuda ta kashe kanta.
Likitocin matar sun shawarci danginta a kan su
bari a yi mata tiyata saboda lokacin haihuwarta
bai yi ba, kuma kan jaririnta ya yi girma da
yawa amma sai suka ki.
Kafar yada labaran China ta ce mijin matar ne
ke son ya ga mai dakinsa ta haihu da kanta
maimakon yi mata aiki.
Sai dai mai nakudar ta gaza jurewa tsananin
ciwo inda ta fado kasa ta tagar asibitin, kuma
ta kashe kanta da jaririn da take dauke da shi.
Batun ya janyo muhawara a shafukan sada
zumuntar China, inda wasu ke tuhuma a kan
dokar da ta ce sai dangin mutum sun amince
kafin a iya yi masa aiki a asibiti.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: