Monday, 11 September 2017
Kasashen da kogin Kwara ya ratsa na cikin barazanar ambaliya

Home › › Kasashen da kogin Kwara ya ratsa na cikin barazanar ambaliya

Hukumomi a jamhuriyar Nijar, sun gargadi
hukumomin Najeriya da na jamhuriyar Benin,
game da barazanar ambaliyar ruwa daga kogin
Kwara, sakamakon karuwar ruwa a kogin.
Wannan gargadi da aka yi na zuwa ne
sakamakon irin barnar da ambaliyar ruwa ke ci
gaba da yi a wasu yankuna na kasashen.
Ko a watannin baya, mutane da dama sun rasa
rayukansu a Nijar a sakamakon faduwar gidaje
da ambaliyar ruwa ta haddasa.
Ministan ma'aikatar kula da afkuwar bala'o'i a
Nijar, Alhaji Lawan Magaji, ya ce, an shirya
kwashe dubban jama'ar da ke zaune a
yankunan da ke gabar kogin Kwara, domin
mayar da su kan tudun mun tsira don gujewa
barnar da ambaliyar ka iya haddasawa.
Garin Tilaberi, na daya daga cikin garuruwan
da kogin Kwara ya ratsa a Nijar,kuma
yawancin jama'ar da ke zaune a garin, ba su
samu labarin kiran da aka yi musu na cewa su
bar gidajensu saboda barazanar ambaliyar
ruwa ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake
fuskantar ambaliyar ruwa wadda ke janyo
asarar rayuka da dukiyoyi a jamhuriyar Nijar da
Najeriya ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: