Wednesday, 6 September 2017
Hare-Haren 'Yan Boko Haram Sun Kashe Dubban Mutane A Yammacin Afrika

Home › › Hare-Haren 'Yan Boko Haram Sun Kashe Dubban Mutane A Yammacin Afrika

Kungiyar dake sa ido akan hakkokin
bil'adama ta ce yin amfani da mata da
yara kanana wajen kai hare-haren
kunar bakin wake na cikin abubuwan da
suka haddasa karuwar mace-macen da
aka samu a 'yan watannin baya.
Kungiyar rajin
Amnesty International ta ce kusan fararen
hula 400 aka kashe a kasashen Kamaru da
Najeriya sanadiyar hare-haren kunar
bakin wake da ‘yan kungiya Boko haram
suka kai tun daga watan Afirilun wannan
shekarar, wanda ya fi linkin hare-haren da
‘yan kungiyar suka kai cikin watanni 5
kafin watan Afrilu.
Wani rahoto da kungiyar ta kare hakkokin
bil’adama ta fidda yau Talata ya ce, akalla
fararen hula 223 mayakan boko haram
suka kashe tun daga watan Afrilu, ciki
harda fararen hula 100 da aka kashe a
watan Agusta kadai. An kuma kai wani
mummunan hari ranar 25 ga watan Yulin
wannan shekarar, lokacin da aka harbe
mutane 40 har lahira a wani kwanton
bauna da mayakan boko haram suka yiwa
wata tawagar masu hakar man fetur a
jihar Borno. Kungiyar Amnesty ta ce ta
yiwu adadin wadanda suka rasa
rayukansu ya fi haka, saboda ta yiwu ba a
sami rahoton wasu hare-haren da aka kai
ba.
A makwabciyar Najeriya kuma, Kamaru,
an kashe akalla fararen hula 158
sanadiyar hare-haren kunar bakin wake
tun daga watan Afrilu, ciki harda harin
bom din da aka kai a wani wurin wasa a
birnin Waza, ranar 12 ga watan Yuli
wanda ya hallaka mutane 16. Kungiyar ta
Amnesty International ta ce ta yiwu
fatattakar ‘yan boko haram da dakarun
Najeriya suka yi daga dajin Sambisa, zuwa
tsaunukan Mandera shi ya kawo karuwar
hare-haren a kasar Kamaru.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: