Sunday, 10 September 2017
Danayu.cf Babban shafin a nahiyar Africa

Home › › Danayu.cf Babban shafin a nahiyar Africa
A ranar Asabar Barcelona ta ci Espanyol 5-0 a
gasar La Liga wasan mako na uku da suka kara
a Camp Nou.
A karawar ce Lionel Messi ya ci kwallo uku
rigis, kuma karo na 38 kenan yana yin haka
tun komawarsa Barcelona da taka-leda a
matsayin kwararren dan kwallo.
Jumulla ya ci kwallo uku sau 27 a gasar La
Liga da kuma sau bakwai a gasar cin kofin
zakarun Turai da sau uku a Copa del Rey da
sau daya a Spanish Super Cup.
Karo na uku kenan Messi dan kasar Argentina
yana cin Espanyol kwallaye uku a wasa, amma
Valencia ce kungiyar da ya fi cin kwallo uku
rigis, wacce ya yi wa hakan sau hudu a tarihi

Share this


Author: verified_user

0 Comments: