Tuesday, 12 September 2017
Buhari Ya Roki Gwamnoni Su Biya Albashi Da Fansho Na Ma'aikatansu

Home Buhari Ya Roki Gwamnoni Su Biya Albashi Da Fansho Na Ma'aikatansu

Shugaba Muhammad Buhari ya roki gwamnonin jihohin kasar nan kan su biya basussukan albashi na ma'aikata da kuma Fansho na wadanda suka yi ritaya inda ya koka kan yadda wasu gwamnoni suka sarrafa kudaden tallafi na Paris Club da aka ba su.

Shugaban ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya karbi bakuncin majalisar sarakunan Arewa inda ya nuna cewa a kullum yana kwana ne da tunanin halin da kasar ne ke ciki musamman ma talaka don haka dole ne gwamnonin su rage masa wasu nauyin.

®Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: