Sunday, 10 September 2017
'Liverpool ba za ta daukaka kara ba kan jan katin Sadio Mane'

Home › › 'Liverpool ba za ta daukaka kara ba kan jan katin Sadio Mane'


Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba za su
daukaka kara ba kan jan katin da aka ba Sadio
Mane inda ya ce "wani karin ba ta lokaci ne,
kamar wasan da suka buga da Manchester
City", in ji jaridar Independent.
Shi ma tsohon wasan Manchester United Rio
Ferdinand ya nuna cewa ya sha aikata irin abin
da Mane ya yi, amma ba a taba yi masa
hukunci irin nasa ba, kamar yadda ya wallafa
wani hoto a shafinsa na Twitter.
Arsenal ta amince da yarjejeniyar sayen
Thomas Lemar daga Monaco a watan Janairu.
Dan wasan Faransar zai kulla yarjejeniyar
shekara biyar ne inda za a rika biyan fam
250,000 a kowane mako, in ji jaridar Daily Star.
Ita ma kungiyar Manchester United ta shirya
neman Leymar, in ji jaridar Sunday Mirror.


Sabon dan wasan Leicester City, Adrien Silva,
yana atisaye da kaninsa saboda yadda ba a
yarda ya yi atisaye da sabuwar kungiyarsa ba
yayin da bar kungiyar Sporting Lisbon, an ki
amincewa ne saboda cinikinsa ya saba wa
dokar hukumar Fifa, a cewar jaridar Leicester
Mercury.
Kungiyar Juventus za ta yi zawarcin dan
wasan Southampton Virgil van Dijk, a watan
Janairu, kamar yadda jaridar Sunday Mirror ta
wallafa.
Atletico Madrid ta tura wata tawaga Chelsea a
ranar Asabar don kammala batun cinikin sayen
Diego Costa daga Chelsean, a cewar jaridar
Sunday Express.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: