Sunday, 10 September 2017
Ankama babban kwamandan IS a kano

Home › › Ankama babban kwamandan IS a kano
Hukumoni a Najeriya sun ce sun kama babban
kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta
yamman wanda ya kisa kai wa Musulmi hari
lokacin bukukuwan babbar sallah.
Hukumar binciken farin kaya ta kasar (DSS) ta
ce kungiyar masu tada kayar baya ta IS reshen
yammacin Afirka (ISWA) ta shirya ta da zaune
tsaye lokacin bukukuwan sallah wanda aka yi
a makon jiya.
Kungiyar ta shirya kai hare-hare a jihohin Kano
da Kaduna da Neja da Bauchi da Yobe da
Borno da kuma babban birnin Tarayya Abuja,
kamar yadda wata sanarwar da hukumar ta
aike wa BBC ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa Husseini Mai-
Tangaran wanda shi ne babban kwamandan
kungiyar shi ne ya kitsa wani mummunan hari
da aka kai a jihar Kano a shekarar 2012.


Har ila yau kungiyar karkashin jagorancin Mai-
Tangaran ita ce ta kai hare-hare da dama a
yankin Arewa-maso-Gasahin kasar wanda
yake ci gaba da fama da rikicin Boko Haram, a
cewar hukumar DSS.
Kwamanda Mai-Tangaran wanda ake nema
ruwa-a-jallo tun a shekarar2012, ya shiga
hannu ne a ranar 31 ga watan Agustan bana a
Kano.
Hakazalika an kama wani mayakin kungiyar
ISWA mai suna Abdulkadir Umar Mohammed a
kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, a cewar
sanarwar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: