Sunday, 10 September 2017
Ana Tuhumar Ministar Harkokin Mata Da Salwantar Da Milyan 12

Home Ana Tuhumar Ministar Harkokin Mata Da Salwantar Da Milyan 12

* Kwamitin Gudanarwar APC Zai Yi Zama Kan Atiku, Aisha Alhassan 


Wasu bayanai da suka fito daga ofishin Babban Mai Bincike na gwamnatin tarayya sun nuna cewa Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan ta salwantar da Naira Milyan 12 wajen yin wata tafiyar sa ido ba bisa ka'ida ba.

Ofishin Babban Mai Binciken ya nemi ,Ministar ta gaggauta mayar da kudaden cikin asusun gwamnatin tarayya. Ana dai ci gaba da ce ce ku ce kan kalaman Ministar wadda ta fito fili ta nuna cewa ba ta tare da Shugaba Buhari a siyasance.

A wani labari makamancin wannan, a ranar Litinin ne, kwamitin zartaswa na Uwar jam'iyyar APC zai yi zama kan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atku Abubakar wanda ya caccaki gwamnatin Buhari da kuma Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan wadda ta marawa tsohon Mataimakin Shugaban baya.

Sources:Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: