Monday, 11 September 2017
An yi arangama tsakanin sojoji da yaran Nnamdi Kanu

Home › › An yi arangama tsakanin sojoji da yaran Nnamdi Kanu

Rundunar sojin Najeriya ta musanta wasu
rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari
tare da kashe mutane a garin Afaraukwu na
madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra,
IPOB, Nnamdi Kanu.
A sanarwar da rundunar ta fitar, ta karyata
labarin da kungiyar ta IPOB take yadawa da
ma wasu hotuna na mutane da ake cewa
sojojin sun harba wadanda ake yadawa a
intanet,a lokacin da sojojin suka yi wa kauyen
Nnamdi Kanun dirar mikiya.
A martanin da sojojin suka yi sun ce babu wani
abu makamancin haka da ya faru, illa dai wasu
tsegarun kungiyar ta fafutukar kafa kasar
Biafran ne suka datse hanya ga kwambar
sojojin da ke kewaya birnin Umuahia na jihar
Abia a ranar Lahadi da yamma, har ta kai da
suna jifan sojojin da duwatsu da fasassun
kwalabe.
Wannan al'amari dai ya yi sanadiyyar raunata
wata mata da ke wucewa da kuma wani kofur
na sojin, in ji sanarwar sojojin.
A dalilin haka ne sojoji suka yi ta harbin iska
don tartatsa mutanen.
Sanarwar ta kuma ce: "Muna so mu gargadi
masu ta da zaune tsaye da su daina yada
karya irin wannan."
"Muna umartar mutane da su fita su yi
sabgogin gabansu kamar yadda suka saba, su
kuma kai rahoton duk wani abu da ba su yarda
da shi ba zuwa ofishin 'yan sanda."
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake
samun fito na fito tsakanin 'yan Biafra da
jami'an tsaron kasar ba.
Ko a watan Nuwambar 2016 ma kungiyar kare
hakki bil'adama ta Amnesty International ta
zargi jami'an tsaron Nigeria da kisan a kalla
masu zanga-zangar lumana 150 a watan
Agustan 2015.
Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan
makamai wajen murkushe masu zanga-zangar
da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso
gabashin kasar.
Sai dai ko a wancan lokacin rundunar sojin ta
musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu
zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron
kasa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: