Wednesday, 6 September 2017
A Jihar Zamfara Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yansanda Uku

Home › › A Jihar Zamfara Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yansanda Uku

Da alama yarjejeniyar da gwamnatin
Zamfara ta cimma tare da 'yan bindiga
dake satar mutane suna yiwa mutane
kwace watannin baya ta rugurguje
saboda yanzu 'yanbindigan sun koma
bakin abun da suka saba yi inda suka
sace yansanda uku a wani kauye jiya din
nan.
Al'amuran kai hare
hare da sace sacen shanu har ma da yin
garkuwa da jama'a na cigaba da addabar
jama'a a jihar Zamfara 'yan watanni
bayan da gwamnatin jihar ta yi wani sulhu
tsakanin Fulani 'yan bindiga da 'yan
bangan yankunan.
Rahotanni sun ce jama'ar wasu kauyukan
sun soma kaura daga gidajensu
musamman a karamar hukumar Tsafe.
Lamarin baya bayan nan dai shi ne
rahoton sace wasu jami'an 'yansanda uku
daga garin Gyeda dake cikin karamar
hukumar Tsafe da yammacin jiya inda
kawo yanzu babu duriyar 'yansandan ko
inda suke.
Wani ganao Haliru Magani yana mai cewa
barayi ne suka je Kyeta suka dauke
'yansanda uku daga nan suka ratsa ta wani
kauyen akan babura bakwai dukansu rike
da bindigogi.
A cewar Haliru mutane na zaman dar dar
koina saboda wannan ba shi ne karo na
farko ba. Daga Gusau zuwa Magami an sha
tare mutane ana kwace masu kudi da kaya.
Malam Haliru yayi mamakin yadda za'a ce
gwamnati ta yi sulhu amma ta bar barayin
da makamansu. Amma an bar mai laiffi da
makami sai ya koma aikinsa,inji Haliru.
Rundunar 'yansandan jihar ta tabbatar da
cewa an yi awan gaba da jami'anta uku a
garin na Kyeta.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da
karin bayani.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: