Saturday, 9 September 2017
A Jihar Bauchi Wata Mata Ta Kashe Jaririn Kishiyarta

Home › › A Jihar Bauchi Wata Mata Ta Kashe Jaririn Kishiyarta

Wata da ta ce an yi mata auren dole ta
kashe jaririn kishiyarta daga bisani
kuma ta yi nadama tana neman gafara.
Kakakin rundunar
'yansandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti
Abubakar shi ya tabbatar da kashe jaririn
da wata mata ta yi tare da yiwa manema
labarai karin bayani.
A cewarsa ranar 19 ga watan da ya gabata
ne a wani kauye dake cikin karamar
hukumar Alkaleri ne a gidan wani
Abdullahi ita matar ta shiga dakin
uwargidan ta dauki jaririnta ta bashi guba.
An kai yaron gidan magani dake kauyan
amma rai yayi halinsa. Yace ita matar da
ta aikata danyen, aikin an kamata tana
hannunsu.
Matar ta amsa laifinta da kanta ba tare da
wani matsi ba. Yanzu 'yansandan na shirin
gurfanar da ita gaban kotu domin a yi
mata hukumci.
A zantawa da manema labarai Malama
Yindatu Abdullahi Ori ta amsa laifinta ta
ce auren dole aka yi mata. Tace babu
zancen kishi akan batun. Tana mai cewa
tsautsayi ya sa ta aikata mummunan aikin.
Ta roki Allah ya yafe mata.
Malama Yindatu tace babu soyayya
tsakaninta da mijinta kuma idan ta fadawa
mahaifinta sai ya koreta amma mijin
wanda ya je aikin hajji ya yi alkawarin
bata takardar saki idan ya dawo.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da
karin bayani.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: