Thursday, 10 August 2017
Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda

Home Kannywood: Sani Danja ya samu muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda
- Masarautar Bidda ta karrama dan wasan Hausa Sani Danja

- Sarkin Bidda Alhaji Yahaya Abubakar ya nada Danja Zakin Arewa

Shahararren jarumin Kannywood Sani Danja ya samu mukamin sarautar gargajiya a masarautar Bidda dake jihar Neja a ranar Asabar 5 ga watan Agustan bana, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mai martaba Sarkin Bidda Alhaji Yahaya Abubakar ne ya nada Sani Danja sarautar gargajiyan, inda ya nada shi sarautar Zakin Arewa, inji majiyar 24wikis

Daruruwan masoya fitaccen jarumin sun yi dafifi a wajen bikin nadin sarautar daya wakana a fadar Sarkin Bidda, inda aka jiyo wata masoyiyarsa, Aisha Yusufu tana fadin nadin sarautar tasa yazo a daidai lokacin daya dace.


“Sani Danja tauraro ne a Kannywood, kuma yana taimaka ma matasa da dama suna cin ma burinsu a fannoni daban daban.” inji Aisha Yusufu.


Mawaki Sani Danja, kuma mai yin shirin wasan kwaikwayo ya samu daukaka a harkar fim da wake wake sakamakon irin rawar dayake takawa, da kuma irin shigar da yake yi.

All Image © Naij

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Gsky mu 'yan arewa bamu yarda da wannan nadin ba,dan a arewa ance wai zakin arewa,mai yayi a arewar inbanda bata tarbiyar al'umma.Dan haka gaskiya bayar d wannan nadinba.Da daima zakin bidda aka na dasa,to wannan sammakal,bama goyan baya d wannan nadin gangamdin.

    ReplyDelete