Sunday, 13 August 2017
Fati Mohammad Ta Zama Daraktar Gidauniyar Atiku Abubakar

Home Fati Mohammad Ta Zama Daraktar Gidauniyar Atiku Abubakar

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Hajiya Fati Mohammad ta zama daraktar harkokin mata na Gidauniyar Atiku, wato 'Atiku Care Foundation' (ACF) reshen jihar Kaduna.

Fati wadda 'yar asalin jihar Adamawa ce, tana daya daga cikin jaruman fim din Hausa da suka shahara a shekarun baya, inda yanzu haka take zama a jihar Kaduna.

Fati wadda ta fito a finafinai irin su Sangaya, Zarge, Marainiya da sauransu, jakada ce a kungiyar UNICEF. Sannan kuma an ba ta matsayin ne duba da yadda ta kasance mai taimakwa marasa galihu.

Takardar da ke dauke da sanarwar matsayin da aka baiwa tsohuwar jarumar, na dauke ne da sa hannun shugaban Gidauniyar Ta Atiku reshen Kaduna, Ibrahim Dahiru Danfulani.


sources:Rariya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: