Sunday, 2 July 2017
Yau Ake Nuna Fim Din Mansoor A Abuja

Home Yau Ake Nuna Fim Din Mansoor A Abuja


Yau Lahadi ne ake nuna fim din Mansoor na Shahararren Kamfanin shirya finafinan Hausan nan, wato FKD Production mallakar fitaccen jarumi Ali Nuhu.

Za a nuna fim din ne a sinimar Genesis Deluxe dake Ceddi Plaza centarl Area dake Abuja da misalin karfe tara na dara (9:00).

Za a sake nuna fim din ne sakamakon wasu da suka zo kallon fim din da dama ba su samu halartar kallon fim a kan lokaci ba. Wanda hakan wata dama ce ga wadanda suke da bukatar kallon fim, wanda aka jima ana daukin zuwan ranar nuna shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: