Saturday, 29 July 2017
Shin Mata 'Yan Fim Karuwai ne Ko masu fadakarwa?

Home Shin Mata 'Yan Fim Karuwai ne Ko masu fadakarwa?

(Gaskiyar magana) Kwana biyu da ya wuce, na yi rubutu game da abinda ya shafi
Adabin Bariki. Na fadi nau'ika na karuwai da rabe raben su. A cikin masu comment akwai
wadanda su ka yi ta tambaya ta, Mata 'yan wasan Hausa fa, suma dole a sako su a jerin rabe
raben karuwan .A kwai wacce ta turo min sakon, gaskiya na yi rashin adalci in har ban sa ka su a jerin karuwai ba.

Ma'anar da na bayar ta karuwa ita ce, wacce ta bar gaban Mahaifanta bisa wani dalili ta
kama daki da zummar kasa hajar da Allah ya hore ma ta. Wasu na ganin Mata 'yan wasan
Hausa ma sun bar gaban Mahaifansu, kuma har sun kama gida .
Da farko niyya ita ce ginshikin kowanne aiki, duk yarinyar da ta baro gaban iyayenta da
niyyar shiga wasan Hausa, ba ta na barowa da niyyar kasa hajar da Allah ya hore ma ta ba ne. Idan ka na ganin ai idan ta kama gida, maza na kai ma ta ziyara, wanda da wannan dalilin ka ke ma ta kallon karuwa.

Me za ka ce da wadanda kan zo karatun jamia, mahaifansu su kama mu su gida su zauna kafin su kammala karatu?
Ya kuma za ka kira maaikaciya da aka yiwa canjin aiki garin da ba na ta ba, ta je ta kama gida? Hujjar ka su na fita location da Maza har a kwana ana shooting, wanda a tunanin ka masha'a ake. Me za ka ce da malamar asibitin da ke kwanan duty tare da Maza?
Me za ka ce da Yar sanda Mace da ke kwana tare da Maza a dutin dare? Ko ka na ganin wasan Hausa ba sana'a ba ce? Ka na da hujjar kiran 'yar wasan Hausa da sunan Karuwa? Ok ina hujja. Wani ya turo min sako, wai in je in duba scandal na Hiyana, wannan karara ya nuna tsantsar rashin adalci da har za'a dauki hukuncin mutum guda a hukunta mutum dubu da shi.

Me za ka ce da matan da kasuwancin saye da sayarwa ke kai su kasashe, su je lafiya su
dawo lafiya? Ko duk karuwai ne a mahangar ka. Domin idan suka je su kan kama daki a Hotel ne su zauna har su gama alamuran su...
Mata 'yan wasan Hausa ba karuwai ba ne, idan kuma ka ce karuwai ne, saboda sun kama gida sun zauna. To fa duk wata daliba ko ma'aikaciya da ta kama gida ta zauna sunanta Karuwa kenan. Idan kuma dalilinka ta na cudanya da Maza, to fa duk wata Daliba ko Maaikaciya sunanta Karuwa a mahangarka.

Wani ya tambaye ni game da mata mawaka, wadannan Case din su mai sauki ne, da damar
su , su na gaban Mahaifan su ne ko shakikan su. Ko da sun kama gidan ne ba sunan su Karuwai ba.
Rubutuwa : Auwal Garba Danbarno

Share this


Author: verified_user

0 Comments: