Tuesday, 4 July 2017
Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

Home Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun Kirsimeti da sabuwar shekara
Gwamnatin tarayya ta bayar da ranekun litinin 25 da talata 26 ga watan Disambar sherarar 2017 da kuma litinin 1 ga watan Janairun 2018 dan yin bukuwan Kirsimeti dana sabuwarshekara, da yake sanarwa a madadin gwamnatin tarayya, ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau yayi kira ga mabiya addinin kirista da suyi amfani da wannan dama wajan yiwa Najeriya addu'ar cigaba.Haka kuma yayi kira ga 'yan Najeriya da suci gaba da bayar da gudummuwa wajan hadin kai da zaman lafiya tsakanin al'umma, ya kuma yi kira da cewa a baiwa gwamnatin shugaba Buhari goyon baya a shirinta na inganta rayuwar 'yan Najeriya.

A karshe ya taya murnar kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: